Kotun Tarayya Ta Ɗage Sauraron Buƙatar Belin El-Rufai Zuwa 31 Ga Wata
Wata Babbar Kotun Tarayya mai zama a Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar ba da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, wato Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga watan Maris.
Tsohon gwamnan ya gurfana a gaban kotun ne a yau Talata, inda ake zarginsa da aikata laifukan hulɗa da kuɗaɗe haramun da kuma karkatar da kadarorin gwamnati zuwa amfanin kansa.
Alƙalin kotun ya bayyana cewa an ɗage sauraron buƙatar belin ne domin ba wa ɓangarorin shari’ar damar kammala shirye-shiryensu kafin ci gaba da zaman kotun.
Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron shari’ar a ranar 31 ga Maris, inda za a yanke hukunci kan batun bayar da beli ga wanda ake tuhuma.
Comments
Post a Comment