Khamenei Ya Gargadi Amurka, Ya Bukaci Rufe Sansanoninta Da Ke Gabas ta Tsakiya
Mojtaba Khamenei ya yi kira ga Amurka da ta rufe dukkan sansanonin sojojinta da ke yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai gargadin cewa za a ci gaba da kai musu hare-hare idan ba a dauki wannan mataki ba.
A cikin jawabinsa na farko ga jama’a, Khamenei ya ce Iran na son kyakkyawar alaka da kasashen makwabta, amma zai ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke cikin kasashen yankin muddin suna nan.
Ya bayyana cewa manufar Iran ita ce matsa lamba ga makiyanta, inda ya ce mashigar ruwan tekun Hormuz za ta cigaba da kasancewa a rufe domin amfani da ita a matsayin wata hanya ta takura wa abokan gabanTehran.
Khamenei ya kuma jaddada cewa Iran za ta ci gaba da gwagwarmaya domin daukar fansar jinin dukkan “shuhada” na kasar, tun daga tsohon jagoran addinin kasar da aka kashe har zuwa kananan yara da suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai.
Haka kuma ya yabawa sojojin kasar bisa rawar da suka taka wajen hana Iran fadawa karkashin ikon kasashen waje ko kuma rarrabuwa. Ya ce gwamnatin kasar za ta samar da tallafin kudi da sauran nau’o’in taimako ga mutanen da suka jikkata ko suka rasa ‘yan uwansu a yakin.
A karshe, Khamenei ya jaddada bukatar hadin kan ‘yan Iran, yana mai kira gare su da su kawar da sabani tare da hada kai domin kare martabar kasar.
Comments
Post a Comment