Kasar Spain Ta Janye Jakadanta Daga Isra’ila


Gwamnatin ƙasar Spain ta sanar da janye jakadanta daga Israel, inda ta ce daga yanzu ofishin jakadancin ƙasar da ke birnin Tel Aviv zai kasance ƙarƙashin jagorancin jami’in diflomasiya na jeka-na-yika.

Rahotanni sun bayyana cewa an wallafa wannan mataki a cikin jaridar gwamnatin Spain mai ɗauke da muhimman sanarwar hukuma. Wata majiya daga ma’aikatar harkokin wajen Spain ta kuma tabbatar da labarin.

Matakin na nufin cewa ofishin jakadancin Spain da ke Tel Aviv ba zai kasance ƙarƙashin cikakken jakada ba a halin yanzu, sai dai wani jami’in diflomasiyya na wucin gadi, wanda zai ke kula da harkokin ofishin har sai an nada sabon jakada ko kuma a sake duba dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Masu lura da al’amuran siyasar ƙasa da ƙasa na ganin cewa irin wannan mataki kan zama wata alama ta nuna rashin gamsuwa ko kuma ƙara matsin lamba a harkokin diflomasiyya tsakanin ƙasashe.

Sai dai har zuwa yanzu gwamnatin Spain ba ta bayyana cikakken dalilin da ya sa ta ɗauki wannan mataki ba, duk da cewa ana ganin yana da alaƙa da tashin hankalin siyasa da ke tattare da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Masana sun ce saukar da matakin wakilcin jakadanci daga jakada kan kasance wata hanya ta nuna cewa dangantaka tsakanin ƙasashen ta fara tsami, amma ba a kai ga katse ta gaba ɗaya ba.

A halin yanzu dai ana sa ran matakin na kasar ta Spain zai iya jawo karin muhawara a harkokin diflomasiyyar Turai game da hulɗar su da Isra’ila.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO