Jami'ar Ahmadu Bello da NIRSAL Sun Shirya Haɗin Gwiwa Domin Bunƙasa Sana'ar Noma

Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, wato (ABU) da Bankin ba da Lamunin ayyukan gona na kasa, Wanda ke karkashin babban Bankin Najeriya, wato (NIRSAL) na shirin kulla haɗin gwiwa domin bunƙasa noman kasuwanci mai ɗorewa a Najeriya.

Shirin haɗin gwiwar ya biyo bayan wata ganawa tsakanin shugabannin manyan cibiyoyin biyu da aka gudanar a birnin Abuja a makon da ya gabata, inda suka nuna aniyarsu ta gina ƙaƙƙarfan haɗin gwiwa a fannin kasuwancin noma.

Jami'ar ABU na da babbar cibiyar noma wadda ba ta da tamka a cikin jami’o’in Najeriya, yayin da NIRSAL kuma wata cibiyar kuɗi ce da aka kafa domin sake fasalta tsarin bayar da lamuni ga harkokin noma, tare da rage haɗarin jarin da masu zuba jari da masu ba da kuɗi ke fuskanta a fannin kasuwancin noma.

Jami’ar ta bayyana cewa tana sa ran karɓar wata tawaga ta ƙwararru daga NIRSAL domin su tantance damar da ABU ke da ita a fannin noma kafin fara wannan haɗin gwiwa.

A yayin taron da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, 4 ga watan Maris, na wannan shekarar, Mataimakin Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya bayyana cewa jami’ar na matuƙar yaba irin gagarumin aikin da NIRSAL ke yi wajen samar da hanyoyin kuɗi da zuba jari a fannin noma.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin Ministan Raya Kiwo na ƙasa, Alhaji Mukhtar Idi Maiha, bisa ba da shawarar cewa NIRSAL ta zama abokiyar haɗin gwiwa mafi dacewa da ABU wajen gudanar da noman kasuwanci.

Farfesa Ahmed ya jaddada shirye-shiryen jami’ar na shiga wannan haɗin gwiwa, yana mai cewa ABU na da katafariyar cibiyar noma da kuma bankin al'umma na microfinance mallakin jami’ar da za su taimaka wajen sauƙaƙa gudanar da wannan shiri.

Ya kuma nuna cewa Cibiyar Bincike kan Samar da Dabbobi ta Ƙasa (NAPRI) da ke cikin jami’ar ita ce wuri mafi dacewa da za a gudanar da wannan harkar kasuwancin noma.

A cewarsa, binciken da masana kimiyya a NAPRI suka yi kan kajin ShikaBrown wata babbar nasara ce a fannin binciken kimiyya, amma kai wannan aikin zuwa kasuwa domin amfanin jama’a na buƙatar ƙarin ƙoƙari da zuba jari.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan manufofin NAPRI shi ne samar da madara ga dukkan yankin Afirka ta Yamma.

“Saboda haka muna buƙatar zuba jari domin cibiyar ta samu damar samar da duk madarar da ake buƙata a yankin, ta yadda za a mayar da shi kasuwanci mai ɗorewa,” in ji shi.

Shi ma Babban Daraktan NIRSAL, Sa’ad Hamidu, ya bayyana cewa duk inda cibiyarsu za ta shiga dole ne a tabbatar akwai tsarin kasuwanci mai anfani.

Hamidu ya nuna shirye-shiryen NIRSAL na yin haɗin gwiwa da jami’ar, yana mai tabbatar da cewa za su duba yadda za su kawo ƙwararru da kuma samar da kuɗin da ake buƙata domin gudanar da aikin.

Ya ce kafin a fara aiwatar da shirin, dole ne tawagar su ta ziyarci wurin da za a gudanar da aikin domin yin cikakken nazari.

Babban Daraktan ya kuma jaddada cewa dole ne a fara gina cikakkiyar alaƙar kasuwanci kafin a kai ga rattaba hannu kan wata yarjejeniya.

Taron ya samu halartar shugabannin sassa daban-daban na NIRSAL, inda Babban Daraktan cibiyar da Mataimakin Shugaban Jami’ar ABU suka jagoranci zaman.

Daga ɓangaren ABU kuwa akwai Daraktan Sashen Haɓakawa da Ilimi na Ƙasa da Ƙasa, Farfesa Muhammad Inuwa Umar-Buratai; Daraktan Harkokin Jama’a, Auwalu Umar; da Mataimakin Daraktan Haɓakawa, Dr. Ahmed Zakaria.

NIRSAL wata cibiyar kuɗi ce da ba banki ba, wadda Babban Bankin Najeriya (CBN) ke da cikakken ikon mallakarta.

An kafa ta ne musamman domin ƙarfafa zuba jari mai sauƙin samu a fannin noma ta hanyar rage haɗarin da ke cikin tsarin ba da kuɗin kasuwancin noma.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO