Isra’ila Ta Zargi Iran Da Amfani Da Makamai Masu Warwatsewa A Sabbin Hare-Haren Makamai Masu Linzami
Sojojin Isra’ila sun zargi Iran da amfani da makamai masu linzami da ke ɗauke da ƙananan bama-bamai masu warwatsewa (cluster warheads) a hare-haren da ta kai kan Isra’ila. An ce Iran ta kaddamar da hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren soji da Isra’ila da Amurka ke kai wa ƙasar tun daga ranar 28 ga Fabrairu.
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa Iran ta yi amfani da wasu nau’in makamai masu linzami da ke warwatsa ƙananan bama-bamai da dama a sararin samaniya kafin su sauka ƙasa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin Isra’ila ya ce an gano amfani da irin waɗannan makamai a wasu hare-haren da aka kai kwanan nan. Ya kara da cewa rundunar sojin na ci gaba da nazari kan lamarin domin gano cikakkun bayanai.
Rahotanni sun ce wasu bidiyoyi da aka ɗauka a wasu sassan Isra’ila sun nuna yadda haske masu yawa suka rika saukowa daga sama zuwa ƙasa a lokaci guda, abin da masana ke ganin alama ce ta amfani da makamai masu warwatsewa.
Makamai irin waɗannan, da ake kira cluster munitions, na buɗewa ne a sararin samaniya sannan su warwatsa ƙananan bama-bamai da dama a faɗin yanki. Wani lokaci wasu daga cikin waɗannan bama-baman kan kasa fashewa nan take, abin da kan iya zama barazana ga fararen hula har bayan yaƙi ya ƙare.
Sai dai har yanzu Iran ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye ba game da wannan zargi.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Iran, Isra’ila da Amurka ke ci gaba da ƙaruwa, lamarin da ke jawo damuwa a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya.
Hashtags:
#Iran #Israila #RikicinDuniya #LabaranDuniya #GabasTaTsakiya
Comments
Post a Comment