Iran Ta Sake Halaka Sojojin Amurka 6 a Harin da ta Kai Kuwait

Gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa sojoji guda shida sun mutu a wani harin da Iran ta kai wa cibiyar ayyukan soji ta Amurka da ke kasar Kuwait a ranar Lahadi. Harin, wanda ya zo a matsayin martani ga hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran kwanakin baya, ya ƙara tunzura rikicin da ya yi kamari a Gabas ta Tsakiya.

A cewar Shelkwatar Sojin Amirka, makamin da Iran ta harba — ko dai roka ko jirgi marar matuki — ya bugi wani gini na wucin-gadi da ake amfani da shi a matsayin wata Cibiya ta ayyuka na musamman. Rahotanni sun nuna cewa ginin ba shi da cikakkiyar kariya, lamarin da ya bai wa aikin harin damar shiga kai tsaye ya haddasa mummunar fashewa.

A farkon sanarwar, Sojin Amurka sun tabbatar da sojoji uku da suka mutu da dama da suka jikkata. Daga bisani, wani daga cikin raunanan sojojin ya rasu, sannan aka gano gawar wasu biyu da ba a hangosu tun farko ba — hakan ya kai adadin zuwa shida.

An bayyana cewa babu jiniya ko gargadi kafin harin, wanda hakan ya sa sojojin da ke cikin ginin ba su samu damar neman mafaka ba. Shaidu sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 9 na safe agogon Kuwait.

Hare-haren da Iran ke kaiwa sun bazu zuwa wasu ƙasashen yankin Gabas Ta Tsakiya, ciki har da Bahrain, Hadaddiyar Daular Laraba, Iraki, da Kuwait — a wani yunkuri na mayar da martani ga jerin hare-haren da Amurka da Isra’ila suka gudanar a baya.

Rahotanni na daban sun nuna cewa cikin ruɗanin kare kai, sojojin tsaron Kuwait sun harbo jiragen yaki guda uku na Amurka (F-15) saboda kuskuren gane su a lokacin tashin hankalin harin Iran. Duk da haka dukkan matukan jiragen guda shida sun tsira bayan sun yi amfani da kujerun fitar gaggawa.

Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa makamin da ya bugi hedikwatar sojin ya samu damar ketare shingen kariya. Ya ce hare-haren sun ƙara “fallasa haɗarin da sojojin Amurka ke fuskanta” a yankin.

Amurka ta ce har yanzu tana ci gaba da manyan hare-haren soja a yankin tare da Isra’ila, duk da rashin da ake fuskanta, kana ta gargadi cewa damar samun ƙarin hasarar rayuka na iya ƙaruwa yayin da rikicin ke ƙara zafi.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO