Iran Ta Kafa Sharadi: Ku Kori Jakadun Amurka da Isra’ila Ko Ku Hakura Da Wucewa Ta Hormuz
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa duk wata ƙasa daga yankin Larabawa ko Turai da ta kori jakadun ƙasashen Amurka da Isra’ila daga ƙasarta za ta samu cikakkiyar damar wucewa ta mashigar ruwan Hormuz daga gobe Laraba.
Wannan sanarwa ta fito ne daga rundunar Iranian Revolutionary Guard Corps (IRGC), wadda ta ce matakin na daga cikin sabbin dabarun da Iran ke amfani da su yayin da rikicin da ke tsakaninta da Amurka da Isra’ila ke ƙara tsananta.
A cikin bayanin da aka watsa ta kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran, rundunar ta bayyana cewa duk wata ƙasa da ta yanke hulɗar diflomasiyya da Amurka da Isra’ila ta hanyar korar jakadunsu za ta samu “cikakkiyar ‘yanci da iko” na wucewa da jiragen ruwa ta wannan muhimmiyar mashigar ruwa.
Muhimmancin Mashigar Hormuz
Mashigar Hormuz na daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya wajen jigilar man fetur da iskar gas. Ana kiyasta cewa kusan kashi ɗaya bisa uku na man fetur da ake jigilar sa ta ruwa a duniya yana ratsa wannan mashiga.
Saboda haka, duk wani rikici ko takunkumi a wannan mashiga kan haifar da tashin farashin mai da girgiza kasuwannin makamashi a duniya.
Rikicin da Ke Tabbata a Yankin
Sanarwar Iran ta zo ne a lokacin da rikicin soja tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila ke ƙara tsananta, lamarin da ya riga ya haddasa tangarda ga zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin Tekun Fasha.
Wasu rahotanni sun nuna cewa jiragen ruwa da dama sun tsaya cak a bakin mashigar yayin da kasashen duniya ke bibiyar yadda lamarin zai kaya.
Masana siyasa sun bayyana cewa matakin na Iran wata dabara ce ta tilasta wa wasu ƙasashe su nisanta kansu daga Amurka da Isra’ila, domin samun damar ci gaba da jigilar man fetur cikin sauƙi ta mashigar Hormuz.
Sai dai har yanzu ba a ga wata ƙasa da ta bayyana aniyarta ta bin wannan sharadi ba, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da kira da a rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Comments
Post a Comment