ICPC Za Ta Gurfanar da Nasir El-Rufai, a Kotu Ranar Talata Kan Zargin Zamba
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Tarayya, wato (ICPC), ta sanar da shirinta na gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ranar Talata mai zuwa.
A cewar hukumar, an shigar da tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan ne tun ranar 18 ga Maris, inda ake zarginsa da aikata laifukan cin zarafin iko, zamba, da kuma yunƙurin samun wata fa’ida ta hanyar da ba ta dace ba.
Majiyoyi sun bayyana wa Zancen Yau 247 cewa bayan sake shi daga hannun hukumar (EFCC) a watan Fabrairu, El-Rufai ya ci gaba da kasancewa a tsare a hannun ICPC bisa umarnin kotu yayin da bincike ke ci gaba.
Haka kuma, wata kotun majistare ta amince da ƙarin kwanaki 14 na tsare shi a ranar 5 ga Maris, lamarin da ya sa aka tsawaita zaman tsarewar tasa fiye da umarnin farko.
A wani ɓangare kuma, tsohon gwamnan ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yana ƙalubalantar sahihancin binciken da aka yi a gidansa da kuma halaccin umarnin tsare shi, yana neman a kare haƙƙinsa na ɗan adam.
Ana sa ran gurfanar da El-Rufai a gaban kotu zai zama muhimmin mataki a shari’ar da ta janyo cece-kuce a fagen siyasar Najeriya, inda wasu ke kira da a gaggauta gurfanar da shi ko kuma a sake shi idan babu hujja.
Comments
Post a Comment