Hare-haren Iran: Mutuwar Soja Na Huɗu Ta Girgiza Amurka
Washington, DC — Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa sojan ta na huɗu ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a lokacin martanin farko da Iran ta kai bayan hare-haren da Amurka tare da Isra’ila suka kai wa ƙasar Iran a makon da ya gabata.
Rahoton ya fito daga jami’an tsaro na Amurka waɗanda suka bayyana cewa sojan ya jikkata ne a lokacin da Iran ta kai hare-hare da makamai masu linzami kan wasu sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya, a matsayin martani kan abin da ta kira “harin ɓarna da Amurka–Isra’ila suka aikata.”
Wannan sabuwar mutuwa ta kawo adadin sojojin Amurka da suka mutu tun lokacin barkewar sabon zagayen rikicin zuwa huɗu, yayin da wasu da dama suke ci gaba da karɓar magani saboda munanan raunuka da suka haɗa da bugun kwakwalwa (TBI), fashewar abubuwa da konewa.
Jami’an tsaro sun ce fiye da sojoji takwas sun jikkata a wannan hari na farko da Iran ta kai, wanda aka bayyana a matsayin babbakiyar alama cewa rikicin na kara ɗaukar zafi.
Iran: “Martani ne kan abin da Amurka da Isra’ila suka aikata”
Iran ta ce hare-haren nata martani ne kai tsaye kan harin da Amurka da Isra’ila suka kai, wanda ya yi sanadin kisa ga jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, lamarin da ya tayar da tarzoma, zanga-zanga da tashin hankali a fadin yankin.
Mahukuntan Tehran sun sha alwashin cewa za su ci gaba da kare ƙasar daga duk wani abu da suka kira “cin mutunci ga ikon Iran.”
A nata bangaren, rundunar Amurka ta bayyana cewa:
“Rashin rayukan jami’anmu ba zai tafi a banza ba. Za mu ɗauki duk matakan kare sojojinmu a ko’ina suke.”
Har yanzu ba a fitar da sunan sabon sojan da ya mutu ba saboda dokokin soja da ake bin su wajen sanar da iyalai kafin bayyanawa ga jama’a.
Comments
Post a Comment