Gwamnatin Zamfara Ta Yi Sauyi A Ma’aikatar Ilimi Ta Jihar

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Malam Wadatau Madawaki, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar ta bayyana.

Sanarwar wadda Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya fitar a ranar Litinin, ta ce gwamnan ya kuma naɗa Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare, Abdulmalik Abubakar Gajam, domin ya riƙa kula da Ma’aikatar Ilimi a matsayin mai kula da ita na wucin gadi nan take.

A cewar sanarwar, Gwamna Lawal ya nuna cikakken amincewa da ƙwarewar Abdulmalik Gajam, yana mai cewa zai tabbatar da ci gaba da daidaito a harkokin ilimi a faɗin jihar Zamfara.

Haka kuma, gwamnan ya gode wa tsohon kwamishinan, Malam Wadatau Madawaki, bisa gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin ilimi a jihar, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO