Gwamnan Zamfara Ya Amince da Biyan Kudin Rijistar Dalibai 25 na Makarantar Lauyoyi

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan kudin rijistar dalibai ashirin da biyar (25) ‘yan asalin jihar da za su halarci Makarantar Horas Da Lauyoyi ta Kasa, Nigerian Law School a zangon karatu na shekarar 2024/2025.

Babbar Sakatariyar Hukumar Ba da Tallafin Karatu ta Zamfara, Rasheedah Liman ce ta fitar da wannan sanarwa inda ta bayyana cewa matakin wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na inganta samun ilimi mai inganci da kuma tallafa wa dalibai masu kokarin cimma burinsu na aikin lauya.

A cewar sanarwar, gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne domin rage nauyin kudade da ke kan daliban da iyalansu, tare da tabbatar da cewa matsalar kudi ba ta hana matasa masu hazaka cika burinsu na samun kwarewa a fannin shari’a ba.

Hukumar ta ce an zabi daliban da za su ci gajiyar wannan tallafi ne bisa ka’idoji da aka tanada domin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma bai wa kowa dama. An kuma bayyana cewa tallafin zai taimaka matuka wajen ba su damar kammala horon da ake bukata domin zama kwararrun lauyoyi.

Gwamna Lawal ya jaddada kudurinsa na ci gaba da fadada damar samun ilimi ga matasa, musamman wadanda ke fitowa daga iyalai marasa karfi, a matsayin wani bangare na manufofin gwamnati na bunkasa jari-hujjar dan Adam da kuma karfafa matasa su bada gudummawa wajen cigaban jihar.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO