Filin Jirgin Sama na Gusau Zai Kawo Arziki Mai Yawa — Sarkin Fulanin Zamfara

Alhaji Shehu Ahmed, Sarkin Fulanin Zamfara kuma tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Maru da Bunguɗu, ya yaba wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa kammala aikin filin jirgin saman garin Gusau, yana mai cewa wannan babban ci gaba ne ga al’ummar jihar.

Sarkin Fulanin ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da ya yi da jaridar Zancen Yau 247, inda ya ce aikin filin jirgin saman wani abin a zo a gani ne da zai kawo ci gaba mai ɗorewa da bunƙasar tattalin arziki a Zamfara.

Ya ƙara da cewa kammala filin jirgin saman zai rage wahalhalun da maniyyata aikin Hajji daga Zamfara da jihohin maƙwabta ke sha, domin a cewarsa, ba za su ƙara zuwa jihohi kamar Katsina da Sakkwato domin tafiya aikin Hajji ba idan filin jirgin saman ya fara aiki yadda ya kamata.

Alhaji Shehu Ahmed ya jaddada cewa wannan muhimmin aiki zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar, inda ya ce ‘yan kasuwa za su samu sauƙin shigo da kayayyaki da sauran hajojinsu cikin sauri, tare da jawo hankalin baƙi da masu zuba jari zuwa Zamfara.

A cewarsa, wannan mataki na daga cikin manyan nasarorin gwamnatin Dauda Lawal, wanda ya bayyana a matsayin shugaba mai jajircewa da ke da kyakkyawar niyya ga cigaban jihar Zamfara.

Daga ƙarshe, Sarkin Fulanin ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da su sake bai wa Gwamna Dauda Lawal damar yin wa’adin mulki na biyu, domin ya ci gaba da aiwatar da ayyukan cigaba da suka shafi rayuwar jama’a.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO