Fargaban Yiwuwar Hare-Haren Gabas-Ta-Taskiya Tsallakowa Afirka Na Dada Karuwa
Yayin da rikicin siyasa da soja ke ƙara ƙamari a yankin Tekun Fasha, rahotanni sun nuna cewa wani muhimmin sansanin sojin Amurka da ke Afirka na iya shiga cikin haɗarin wannan rikici.
Sansanin sojin na Amurka mai suna Camp Lemonnier, wanda ke cikin ƙasar Djibouti, shi ne kadai sansanin sojin Amurka na dindindin a nahiyar Afirka. Sansanin yana kula da mashigar ruwan Bab el‑Mandeb, wadda ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin kasuwanci mafi muhimmanci a duniya.
Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa kusan kashi 12 cikin 100 na dukkan kasuwancin duniya na ratsa wannan mashiga ta ruwa, wanda ke haɗa Tekun Ja da Tekun Aden, tare da sauƙaƙa zirga-zirgar jiragen ruwa daga Turai zuwa Asiya da Afirka.
Rahotanni sun ce duk da cewa an fi mayar da hankali kan hare-haren Iran a yankin Tekun Fasha, ana ganin an yi watsi da yiwuwar hatsari a wannan yankin na Bab el‑Mandeb Strait. Ana zargin mayaƙan Houthi na kasar Yemen, waɗanda ake dangantawa da goyon bayan Iran, na da makamai masu linzami da za su iya kai hari zuwa yankin.
Idan har aka samu tangarda ko hare-hare a wannan mashiga ta ruwa, masana tattalin arziki na gargadin cewa hakan na iya haifar da tashin farashin mai da kayan abinci a kasashe da dama na Afirka.
Kasashe irin su Masar zuwa Nairobi a Kenya na iya fuskantar hauhawar farashi, saboda yawancin kayayyaki da man fetur na ratsa wannan hanya kafin su isa kasuwannin yankin.
Masana harkokin sufuri da kasuwanci sun ce idan aka samu matsala a Mashigar Bab el‑Mandeb, hakan na iya zama sabon babban kalubale ga tattalin arzikin duniya, musamman ga kasashen Afirka da ke dogaro da shigo da mai da abinci daga waje.
A halin yanzu dai, jami’an tsaro na Amurka da kawayenta na ci gaba da sanya ido kan al’amuran yankin, domin kauce wa duk wani rikici da ka iya dagula zirga-zirgar jiragen ruwa a wannan muhimmiyar mashiga ta duniya.
Comments
Post a Comment