El-Rufai: DSS Ta Tasa Keyar Jami'ai 5 Zuwa ICPC
Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama wasu jami’an ’yan sanda, da na shige da fice, da Kuma na tsaron filin jirgin sama saboda zargin da ake yi na ba da gudunmawa wajen shigowar tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, cikin Najeriya ba tare da hukumomi sun iya kame shi ba.
Wannan mataki ya biyo bayan binciken da DSS ta gudanar kan take-tsaron da ya faru a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, a ranar 12 ga Fabrairu, 2026, lokacin da El-Rufai ya dawo daga ƙasar Masar.
Rahotanni sun nuna cewa an kama jami’ai biyar, ciki har da jami’an ’yan sanda, da jami’an shige da fice, jar da jami’in DSS, sannan da jami’an tsaron jirgin sama (AVSEC)
Ana zargin jami’an da karya ka’idojin tsaro, da karɓar wasu nau’o’in alfarma ko rashawa da kuma amfani da hanyoyin da ba su dace ba domin ba wa El-Rufai damar tsallake shingen tsaro, tare da hana wasu jami’an DSS aiwatar da umarnin kama shi
Bayan kame su, an mika lamarin ga ICPC domin ci gaba da bincike da gurfanarwa.
Tushen Matsalar
Tun bayan dawowar El-Rufai daga Masar, an yi yunkurin kama shi a filin jirgi — lamarin da ya jawo cece-kuce. A wancan lokaci, aka karɓe fasfo ɗinsa, abin da lauyoyinsa suka ce ya saba wa doka.
Akwai rahotanni da ke cewa babu takardar kama shi kai tsaye da ta isa hannun jami’an da ke bakin aiki lokacin.
A gefe guda, El-Rufai na fuskantar wasu bincike da dama, ciki har da, zargin almundahana lokacin da yake gwamna, da zargin mallakar kayan leƙen asiri a gidansa — zargi da iyalinsa da masu goyon bayansa suka karyata
Yanzu haka yana ci gaba da zama a tsare umarnin kotu yayin da ake cigaba da shari’a.
Kame jami’an tsaro da dama a lokaci guda ya kuma haifar da tambayoyi kan, tsaro da gaskiya a filayen jiragen sama, da yiwuwar lalacewar tsarin tsaro, da kuma tasirin siyasa a shari’ar El-Rufai
Hukumomi sun ce bincike na ci gaba, kuma za a ɗauki matakin da ya dace idan an gano ƙarin laifuka.
Comments
Post a Comment