China Ta Goyi Bayan Iran, Ta Gargadi Amurka da Isra’ila Kan Faɗaɗar Rikicin Gabas ta Tsakiya

Rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Iran, Seyed Abbas Araghchi, inda ya jaddada goyon bayan Beijing ga Tehran wajen kare ikon ƙasarta da martabarta.

Rahotannin sun kara da cewa, Wang Yi ya bayyana cewa China na goyon bayan Iran wajen kare ‘yancinta, tsaron ƙasarta, cikakken ikon mallakar ƙasa da kuma mutuncin ƙasa. Ya kuma jaddada cewa Beijing na mara wa Iran baya wajen kare haƙƙoƙinta da muradunta na halal a matakin ƙasa da ƙasa.

An ce Ministan ya kuma yi kira ga kasashen Amurka da Israel da su dakatar da duk wani farmakin soja cikin gaggawa domin kauce wa ƙarin tashin hankali a yankin.

A cewarsa, ci gaba da hare-haren na iya haddasa yaɗuwar rikici zuwa sauran ƙasashen yankin Asia ta Yamma, lamarin da zai iya jefa yankin cikin mummunan rikici mai faɗi.

Wang Yi ya tabbatar cewa China na goyon bayan hanyoyin diflomasiyya da tattaunawa domin warware rikice-rikice, yana mai kira ga ɓangarorin da abin ya shafa da su nuna hakuri tare da komawa kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Wannan tattaunawa na zuwa ne a daidai lokacin da tashin hankali ke ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, inda kasashe da dama ke nuna damuwa kan yiwuwar faɗaɗar rikicin.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO