Babban Kwamandan Tsaron Isra’ila Tomer Bar Ya Rasa Ransa a Harin Iran

A sabon abin mamaki da ya girgiza bangaren tsaro na ƙasar Israel, rahotanni sun tabbatar da cewa Iran ta kashe babban kwamandan sojin sararin samaniyar ƙasar, Tomer Bar, a wani rukon kai da aka kai yau.

Tomer Bar ya kasance ɗaya daga cikin manyan jami’an tsaro masu yanke shawara kan tsare-tsaren yaƙin Isra’ila, musamman a bangaren rundunar sojin saman ƙasar. Mutuwarsa na nuna babban gibi ga hukumar tsaro ta Isra’ila, duba da irin nauyin da yake ɗauka a manyan matakai.

Rahotanni daga bangaren tsaro sun ce wannan hari na Iran ya ƙara dagula lamarin rikicin da ya riga ya yi zafi tsakanin ƙasashen biyu. Masana tsaro na cewa hakan na iya haifar da sabuwar kafaɗa da kai tsakanin rundunonin sojin kasashen.

Alamu na nuna cewa Iran ba ta kammala martaninta ba, domin jami’an tsaron ƙasar sun ce “dukkan waɗanda ke da alhakin matsin lamba kan al’ummar Iran za su fuskanci sakamakon aikinsu, daya bayan daya.”

Daga abin da ke faruwa yanzu, ana sa ran iya yiwuwa Iran za ta ci gaba da kai hare-hare kan manyan shugabannin tsaro na Isra’ila a yau.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO