ASUU Ta Umurci Mambobinta Su Dakatar da Koyarwa Saboda Jinkirin Albashi
Kungiyar Malaman Jamiyoyi ta ASUU ta fitar da sabuwar sanarwa wacce ta umarci mambobinta su dakatar da shiga aji nan take, sakamakon ci gaba da jinkirin biyan albashin wannan watan gwamnati ta yi.
A cikin sanarwar da sakataren ƙungiyar, Hassan Bala, ya sanya wa hannu, ASUU ta tunatar da cewa a zaman majalisar da ta gudanar ranar 28 ga Mayu, 2025, ’yan ƙungiyar sun yanke hukuncin cewa duk lokacin da gwamnati ta gaza biyan albashi bayan kwana uku na fara sabon wata, malaman na jamiyoyin kasar za su dakatar da koyarwa har sai an biya su.
Sanarwar ta ce duk da wannan matsaya ta baya, gwamnati ta ci gaba da jinkirin biyan hakkokin malamai, lamarin da kungiyar ta bayyana a matsayin rashin mutunta ma’aikata da kuma barazana ga tsarin ilimi.
“Muna tuna wa 'yan kungiyar cewa a duk lokacin da gwamnati ta gaza biyan albashi har sabon wata ya kai kwana uku, kada malamin da ya sake shiga aji da sunan koyarwa har sai gwamnati ta biya albashi.” in ji sanarwar.
ASUU ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin kare martabar malamai da tabbatar da cewa gwamnati na mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma.
Sanarwar ta ƙara da cewa daga yau, hudu da wata, 'yan kungiyarta su dakatar da shiga aji, har sai an biya albashi.
Masanan harkar ilimi sun yi gargadi cewa wannan mataki na iya jefa harkokin manyan makarantu cikin wani sabon tsaiko, musamman a lokacin da ɗalibai ke ci gaba da fama da dogayen hutu saboda rikice-rikicen tsakanin gwamnati da kungiyar ta ASUU.
Comments
Post a Comment