APC Ta Samu Sabbin Mambobi 60,987 Cikin Kwana Uku Bayan Sauya Sheƙar Gwamnan Zamfara

Yawan 'yan jam’iyyar  (APC) a Jihar  Zamfara ya karu zuwa 158,697, kwanaki uku kacal bayan sake bude shafin rajistar mambobi ta yanar gizo biyo bayan sauya sheƙar Gwamnan jihar, Dauda Lawal, zuwa jam’iyyar.

Wannan bayani na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara ya fitar a ranar Lahadi a Gusau.

A cewar sanarwar, Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya jagoranci duba yadda ake gudanar da rajistar mambobin ta yanar gizo a cibiyoyi shida da ke Gusau da kuma ƙaramar hukumar Bungudu.

A yayin ziyarar sa, SSG ya samu rakiyar Kwamishinan kula da harkokin Kananan Hukumomi da Sarautu, Injiniya Ahmad Garba Yandi, da kuma Ko’odinetan rajistar na jihar, Hon. Naziru Ibrahim, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

Malam Nakwada ya bayyana gamsuwa da yadda magoya bayan Gwamna Lawal suka fito da yawa domin yin rajista da jam’iyyar APC, lamarin da ya ce na nuna irin goyon bayan da jama’a ke bai wa matakin sauya sheƙar gwamnan.

Sanarwar ta ce cikin kwanaki uku da sake bude rajistar, sabbin mambobi 60,987 sun yi rajista, wanda ya kara da 97,710 da aka riga aka yi wa rajista kafin shigar Gwamna Lawal jam’iyyar, lamarin da ya kai jimillar mambobin APC a jihar zuwa 158,697 zuwa karfe 7:30 na yammacin ranar 15 ga Maris, 2026.

Haka kuma an bayyana cewa a matsakaici, kusan mutane 20,329 ke yin rajista a kullum, abin da jami’an jam’iyyar suka ce na nuna irin karfin tasirin Gwamna Lawal a matakin ƙasa da kuma yadda APC ke kara samun karbuwa a jihar Zamfara.

Sakataren Gwamnatin ya bayyana kwarin gwiwa cewa jam’iyyar za ta cimma sabon burin da ta sa na yawan mambobi kafin wa’adin 25 ga Maris, idan aka ci gaba da wannan turba.

A yayin ziyarar da ya kai Bungudu, Malam Nakwada ya kuma shirya wata ganawa ta yanar gizo tsakanin sabbin mambobin da Gwamna Lawal, wanda a halin yanzu yake a ƙasar Saudi Arabia domin gudanar da Umrah.

Da yake jawabi a yayin ganawar, Gwamna Lawal ya yaba da jajircewar magoya bayansa bisa yadda suka fito da yawa domin yin rajista duk da tsananin zafi da kuma kasancewar ana cikin azumi.

Ya kuma tabbatar musu cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru domin kare muradun al’ummar jihar Zamfara tare da bunkasa ci gaban jihar.

Sanarwar ta samu sa hannun Suleman Ahmad Tudu, Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai ga Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO