Amurka Ta Tura Babban Jirginta Na Bomber B-1 Zuwa Birtaniya Don Kai Hari Kan Iran
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi kakkausar gargaɗi ga ƙasar Iran inda ya ce za ta fuskanci mummunan hari “mai ƙarfi matuƙa” a yau idan rikicin da ke tsakaninsu ya ƙara tsananta.
Trump ya bayyana cewa jirgin yaƙi mafi ƙarfi na Amurka, wato B-1 Lancer — wanda ake yi wa lakabi da “The Bone” — zai iya kai hari domin “cikakken hallaka da mutuwa tabbatacciya”.
Rahotanni sun ce rundunar sojin saman Amurka ta tura wannan jirgin yaƙi zuwa Birtaniya, matakin da ake kallon sa a matsayin shirye-shiryen sabbin hare-hare kan Iran.
Jirgin B-1 Lancer yana daga cikin manyan jiragen yaƙi mafi haɗari a rundunar sojin saman Amurka. Tsawonsa ya kai kafa 146, yayin da fikafikansa ke da tsawon kafa 137.
Haka kuma, jirgin na iya tashi da gudun da ya haura mil 900 cikin sa’a guda, abin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin jiragen yaƙi mafi sauri a rundunar sojin saman Amurka.
Jirgin na iya ɗaukar makamai masu linzami har guda 24 tare da wasu makamai da nauyinsu ya haura tan 34, wanda ke ba shi damar kai hari kan wurare da dama a lokaci guda.
Bugu da ƙari, jirgin yana da na’urorin zamani na gano hari da tsarin GPS, tare da na’urorin karkatar da wata na'urar Mai hangen nesa da kuma kariyar yaudarar makamai, domin shiga sararin samaniya mai tsananin kariya ba tare da an dakatar da shi ba.
A baya, Amurka ta yi amfani da jirgin B-1 Lancer a manyan hare-haren yaƙi a ƙasashen Syria, Libya, Afghanistan da kuma Iraq.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa isowar wannan jirgin zuwa Birtaniya na nuna ƙarin tsaurara matakin soji da Amurka ke ɗauka yayin da rikicin siyasa da na soji tsakanin Washington da Tehran ke ƙara tsananta.
Comments
Post a Comment