Amurka ta Kai Babban Farmaki Kasar Ecuador

Gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa ta fara gudanar da ayyukan soji tare da Ecuador domin kai farmaki kan manyan kungiyoyin safarar miyagun kwayoyi da kuma waɗanda Amurka ta ayyana a matsayin kungiyoyin ta’addanci a ƙasar.

A cewar bayanan da Cibiyar Dakarun Sojin Amurka da ke Kudancin Amurka wato SOUTHCOM ta fitar, dakarun Amurka da na Ecuador suna aiwatar da haddin gwiwar Kai farmaki a sassan ƙasar, musamman wajen dakile ayyukan da ake alakantawa da manyan ƙungiyoyin laifi irin su Los Lobos da Los Choneros, waɗanda suka yi kaurin suna wajen aikata manyan laifuka da tayar da tarzoma.

Ayyukan sun fara ne a ƙarƙashin sabuwar dabarar tsaro. Rahotanni sun bayyana cewa an kaddamar da hare-haren ne bisa sabon matakin da shugaban Ecuador, Daniel Noboa, ya ɗauka domin mayar da martani kan tashin hankalin da ya dabaibaye ƙasar sakamakon ƙaruwa da tashin hankali na ‘yan ta’adda da masu safarar kwayoyi.

A cikin wani faifan bidiyo da SOUTHCOM ta saki, an nuna jirage masu saukar ungulu da dakaru suna gudanar da atisayen yaki, ko da yake har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan wuraren da aka kai farmaki ko irin nasarorin da aka samu ba. Ma’aikatar Tsaron Ecuador wato SOUTHCOM ta ce duk cikakken bayanin yana cikin matakin sirri saboda bukatar tsaro.

Amurka ta nuna cewa Ecuador ta zama babbar hanyar wucewa ga kusan kashi 70 na hodar iblis da ake fitarwa daga kasashen Peru da Colombia zuwa kasuwannin Turai da Amurka. Wannan ne ya sa kasar ta ƙara alakanta ƙungiyoyin safarar miyagun kwayoyi da ayyukan ta’addanci.

Wani Jami’in SOUTHCOM, Janar Francis L. Donovan, ya ce haɗin gwiwa da Ecuador wani mataki ne na ƙarfafa tsaro a yankin, yana mai cewa manufar ita ce rage ikon kungiyoyin da ke janyo rikice-rikice a yankin Amurka ta Kudu.

Masu sharhi sun bayyana wannan mataki a matsayin faɗaɗa rawar da Amurka ke takawa a yankin, kasancewar a baya galibi tana takaita aikace-aikacenta ne ga bincike, bayanan leƙen asiri da kuma farmakin ruwa kan jiragen masu safarar miyagun kwayoyi.

Yanzu dai, wannan shi ne karo na farko da Amurka ta shiga irin wannan gagarumin hadaka na ƙasa da kasa tare da kasar Ecuador cikin irin wannan nau'i, lamarin da wasu ke ganin zai iya haifar da sabbin matsalolin siyasa, yayin da wasu kuma suka yabawa kokarin saboda tsananin rikicin tsaro da Ecuador ke fuskanta.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO