Amnesty International Ta Bukaci Najeriya Ta Dakatar da Tursasa wa Masu Sukar Amurka da Isra’ila

Kungiyar Kare Hakkin BilAdama ta duniya, wato Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya da su dakatar da abin da ta bayyana a matsayin matakan tursasawa da ake dauka kan mutanen da ke sukar gwamnatocin ƙasashen Amurka da Israilal musamman a shafukan sada zumunta.

A cikin wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar a ranar 13 ga Maris, ta ce tana matukar damuwa da yadda jami’an leken asiri na farin kaya wato (DSS) ke matsa lamba kan masu bayyana ra’ayoyinsu game da yakin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar ta bayyana cewa akalla mutane biyu da ke zaune a Kaduna an tsare su, inda ta ce daya daga cikinsu na fuskantar yiwuwar shari’a da ta kira “ta bogi" bisa zargin da ba su da tushe.

Har ila yau, Amnesty ta ce ta samu rahotanni cewa wasu mutane da suka soki gwamnatocin Amurka da Isra’ila ana gayyatarsu zuwa ofisoshin DSS domin yi musu tambayoyi.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta yi gargadin cewa irin wadannan matakai na iya kawo cikas ga kare hakkin dan Adam tare da rage amincewar jama’a da cibiyoyin gwamnati.

Ta kara da cewa sukar manufofin kowace gwamnati ko shugabanninta na daga cikin ‘yancin fadin albarkacin baki wanda kundin tsarin mulkin Nigeria na shekarar 1999 ya tanada, tare da yarjejeniyoyin kasa da kasa na kare hakkin dan Adam da kasar ta rattaba hannu a kai, ciki har da yarjejeniyar Afirka kan ‘yancin dan Adam da al’umma.

A cewar kungiyar, ya kamata hukumomin Najeriya su dakatar da duk wani mataki na takura wa masu sukar gwamnati muddin suna amfani da hakkinsu na fadin albarkacin baki cikin lumana.

Sanarwar ta kara da cewa idan aka ci gaba da daukar mataki kan mutanen da ke sukar gwamnatocin Amurka da Isra’ila, hakan na iya haifar da yanayi na tsoro da zai hana mutane bayyana ra’ayoyinsu a cikin al’umma.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da kare ‘yancin fadin albarkacin baki na kowa, a yanar gizo da kuma a zahiri, tare da kaucewa daukar matakan da za su hana mutane sukar gwamnatocin kasashen waje.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO