Yanda Ƴan Bindiga Suka Kai Hari Masallaci a Kebbi, Suka Kashe Mutum Biyar

Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne sun kai hari a Masallacin Dadinkowa da ke karamar hukumar Maiyama a jihar Kenbi, a ranar Laraba, inda suka kashe mutum biyar tare da jikkata uku.

Rahoton NAN ya nuna cewa maharan sun afka wa masallacin ne yayin sallar magariba, inda suka bude wuta kan masu ibada.

Harin ya biyo bayan yunkurin kwanton bauna da suka yi wa ayarin wani babban hafsan sojin Najeriya mai mukamin Janar a kwanakin baya, wanda bai yi nasara ba – lamarin da ake ganin ya tayar musu da hankali.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin na iya kasancewa ramuwar gayya bayan kaye da maharan suka sha a hannun sojoji.

Jami’an tsaro sun tsaurara matakan tsaro a yankin yayin da ake ci gaba da bincike.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO