Trump Ya Umurci Hukumomin Amurka Su Fara Sakin Takardun Gwamnati Kan Aljanu
A cewar shugaban, wannan mataki zai shafi hukumomi da dama ciki har da Ma’aikatar Tsaro da manyan hukumomin leƙen asiri domin tattara bayanan da ke cikin kundin gwamnati da suka shafi:
- Hangen abubuwan da ba a iya tantancewa ba (UFO/UAP)
- Duk wata shaida ko bincike da aka yi kan yiwuwar rayuwar halittu a wasu duniyoyi
- Da kuma duk wasu bayanai da ake tunanin gwamnati ta ɓoye.
Wannan umurni na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ƙasa ya yi furuci a wani shirin tattaunawa cewa “rayuwar halittu a sararin samaniya tabbas tana yiwuwa”, ko da yake ya ce bai taɓa ganin wata shaida ta cewa Amurka ta taɓa haɗuwa da su ba. Trump ya yi zargin cewa Obama ya “fallasa bayanan sirri”, duk da cewa bai fayyace inda take zargin ya samo asali ba.
Hukumomin tsaron Amurka dai sun dade suna tattara bayanai game da UFO/UAP, inda rahotanni na baya-bayan nan suka nuna cewa yawancin abubuwan da aka gani ana iya dangantawa da:
- Ƙwallan sintiri;
- Na’urorin leƙen asiri;
- Ko abubuwa na fasahar ɗan adam.
Sai dai har yanzu akwai wasu bayanai da ba a bayyana su ba, lamarin da ya sa al’umma da wasu ‘yan majalisa ke matsa lamba a kan a buɗe komai domin ganin gaskiya.
Masu sukar matakin sun ce sau da dama irin wadannan “bayyana bayanai” ba sa fitowa da wani sabon abu, yayin da magoya bayan shugaban ke ganin matakin “ya dace kuma ya jima yana jira”.
Har yanzu ba a bayyana takardu nawa za a saki ba, ko wane ɓangare na bayanan za a bayyana ga jama’a, amma gwamnatin Trump ta ce aikin “ya riga ya fara” kuma za a ci gaba da sanar da jama’a idan akwai sabbin bayanai.
Comments
Post a Comment