Trump Ya ce Yana Fatan Shiga Aljanna
A wani sabon jawabi da ya jawo ce-ce-ku-ce, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana abin da yake tunanin zai iya zama dalilin da zai kai shi Aljanna bayan mutuwa. Wannan jawabi nasa ya fito ne a taro na 74 na addu'o'in kasa, babban taron addu’a da ake shiryawa duk shekara a birnin Washington D.C.
A yayin da yake magana a gaban shugabanni, limamai da manyan jami’an gwamnati, Trump ya ce ya yi abubuwa masu yawa da ya ke ganin alheri ne ga kasarsa da al’umma, kuma watakila hakan ya isa ya zama dalilin shiga Aljanna. Sai dai ya yi gaggawar jaddada cewa bai taɓa kiran kansa cikakken nagari ba — amma yana ganin ya yi aikace-aikace masu muhimmanci.
Ya kuma soki shugabannin da suka gabace shi, yana mai cewa ba su bai wa addini muhimmanci kamar yadda ya yi ba, tare da jaddada cewa a wannan zamanin addini yana dawowa da karfi a Amurka. “Amurka dole ta kasance kasa guda karkashin Allah,” in ji shi.
A gefe guda kuma, Trump ya yi barkwanci da cewa wasu lokuta ma shi kansa ba ya da tabbacin ko zai shiga Aljanna, duk da irin ayyukan da yake yi. Wannan ya sa mutane da dama suka fara tattaunawa a kafafen sada zumunta, wasu na ganin maganarsa wata dabara ce ta siyasa, yayin da wasu ke kallon ta a matsayin tunanin mutum game da rayuwa bayan mutuwa.
Trump dai a baya ya danganta yuwuwar shiga Aljanna da irin abubuwa da yake shirin yi, ciki har da kawo karshen rikicin Ukraine. Amma daga baya ya ce “ban san ko akwai wani abu da zai iya tabbatar min da shiga Aljanna ba.”
Kalaman shugaban sun ci gaba da jan hankalin Amurkawa, musamman mabiya addini, yayin da ake ci gaba da nazari kan yadda yake amfani da batutuwan addini a yakin neman zabensa.
Comments
Post a Comment