TINUBU YA NADA AMB. ISMAIL A MATSAYIN SHUGABAN HUKUMAR JINDADIN ALHAZAI TA KASA

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambassador Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaban kuma Babban Darakta na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON).

Wannan naɗi dai zai fara aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi, kamar yadda sashe na 3(2) na Dokar kafa NAHCON ta 2006 ya tanada.

A cikin wasiƙar da Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, a yau Laraba, ya nemi majalisar da ta gaggauta tantancewa tare da tabbatar da Amb. Yusuf domin ya maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a farkon makon nan bayan shafe watanni 14 yana rike da madafun iko.

Ambassador Ismail Abba Yusuf gogaggen ɗan diflomasiyyar Najeriya ne, wanda ya yi aiki a matsayin Jakadan Najeriya mai cikakken iko a Jamhuriyar Turkiye daga 2021 zuwa 2024.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsara Manarori, a ranar 11 ga Fabrairu, 2026.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO