Sojojin Amurka 100 Sun Sauka a Bauchi

Hukumar tsaro ta ƙasa ta Najeriya, , ta tabbatar da isowar kusan sojojin Amurka 100 tare da kayan aikin yaƙi a filin jirgin sama na Bauchi, domin tallafa wa rundunar sojin Najeriya a yaƙi da 'yan ta’adda.

Bayanin, wanda aka fitar a yau Litinin, ya nuna cewa zuwan sojojin Amurkan ya biyo bayan roƙon gwamnatin tarayya, inda ƙasar Amurka ta amince ta turo ƙwararrun masu horo domin inganta dabarun yaƙi, bincike da kuma musayar bayanan leken asiri.

A cewar Shelkwatar tsaron Kasa, sojojin Amurkan ba za su shiga yaƙi kai tsaye ba, sai dai za su ba da horon musamman, fasaha da tallafin kayan aiki ga dakarun Najeriya domin ƙarfafa su a faɗa da ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP.

Rahotanni sun ce jiragen saman sojojin Amurka sun sauka da misalin karfe goma na safe, inda aka sauke kwamandoji da manyan kayan aiki na musamman da ake amfani da su wajen horo da atisaye.

Masu sharhi kan tsaro sun bayyana wannan mataki a matsayin babban ci gaba a dangantakar tsaron ƙasashen biyu, musamman ganin yadda Najeriya ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa haɗin gwiwar zai taimaka wajen hanzarta dabarun yaƙi da kuma kare rayuka da dukiyoyi, musamman a yankunan da rikice-rikice suka yi kamari.

Tuni dai zuwan sojojin ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, yayin da wasu ke ganin matakin na da amfani, wasu kuma na tambayar ko hakan zai yi tasiri sosai wajen magance matsalar tsaro.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO