Palmer Ya Kafa Tarihi a Premier League Bayan Zura Kwallaye Uku sau Uku a Rabin Farko
A cewar alkaluman hukuma, babu wani ɗan wasa a tarihin Premier League da ya taba cimma wannan bajintar, wanda ke kara ƙara darajar Palmer a matsayin ɗaya daga cikin matasan da suka fi tashe a gasar.
Palmer, wanda ya koma Chelsea daga Manchester City, ya kasance ginshiƙi a tsarin kai hare-hare na tawagarsa, inda yake nuna nagarta wajen ɗaukar nauyi, sarrafa kwallo da kuma sakar waƙar raga ba tare da gajiyawa ba.
Masu sharhi da dama sun yaba da irin yadda wannan matashin ke taka leda, inda wasu ke cewa yanzu ya koma cikin sahun ‘yan wasa mafi tasiri a bana. Masu kallo kuma suna ganin cewa Chelsea na amfana ƙwarai daga bullar wannan sabon tauraro da ke ci gaba da haskakawa a Premier League.
Chelsea da masoyanta za su ci gaba da sa ran ganin Palmer na cigaba da taka rawar gani a sauran wasannin da suka rage na kakar.
Comments
Post a Comment