Nigeria Ta Shiga Kasuwar Halal Ta Dala Tiriliyan 7.7 — Majalisar Dattawa Ta Jinjina wa Tinubu
A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa, ya fitar, ya ce kaddamar da tsarin tattalin arzikin halal “mataki ne mai muhimmanci da ya dace da irin wannan lokaci,” musamman a yayin da gwamnati ke kokarin habaka kudaden shiga marasa alaka da man fetur, kirkirar ayyukan yi, da tallafawa masana’antu da kananan kamfanoni.
Sanata Musa ya ce kasashe da dama irin su Malaysia, Saudiyya, UAE, Burtaniya da Kanada sun dade suna cin gajiyar tattalin arzikin halal, wanda ya kunshi bangarori da dama kamar abinci, magunguna, kayan kwalliya, yawon bude ido da kuma lamunin kudi bisa ka’idojin halal. Ya ce Najeriya ma tana da duk wata baiwa da za ta iya zama jagora a wannan fannin saboda arzikin noma, yawan jama’a, masana’antu masu tasowa da kuma bangaren ayyukan zamani.
Kwamitin ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa ganin muhimmancin wannan kasuwa ta duniya, yana mai cewa sabuwar tsarin halal din ya yi daidai da muradun gwamnatin sa na fadada fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, habaka kudaden shiga, da karfafa tattalin arzikin kasa.
A wajen kaddamar da shirin a Fadar Shugaban Kasa a Abuja a ranar 6 ga Fabrairu, 2026, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya wakilci shugaban. Shirin dai ya samo asali ne daga hadin gwiwa da Najeriya ta kulla da Halal Products Development Company na Saudiyya tun a taron Makkah Halal Forum na 2025.
Kwamitin Kudin Majalisar Dattawa ya yi alkawarin bayar da cikakkiyar gudunmuwar da ta shafi dokoki, sa ido, da tabbatar da ingantaccen tsarin da zai sa a aiwatar da wannan sabon tsari cikin nasara.
Masana sun yi hasashen cewa tsarin tattalin arzikin halal na iya kara wa Najeriya darajar dala biliyan 1.5 nan zuwa 2027, tare da samar da karin kudaden shiga da damar zuba jari a shekaru masu zuwa.
Comments
Post a Comment