Matasa Sun Kona Barawon Waya Har Lahira a Kano

A unguwar Dorayi da ke cikin birnin Kano, wasu fusatattun matasa sun banka wa wani da ake zargin barawon waya wuta, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da tayar da kura kan matsalar daukar doka a hannu.

Wasu daga mazauna unguwar da suka yi wa jaridar ZANCEN YAU247 jawabi ta wayar tarho sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan da matasan suka cafke mutumin da ake tuhuma da kwacen jakar wata matashiya sannan Kuma ya daba ma ta wuka a jijiyar wuya a unguwar. 

Maimakon mika shi ga jami’an tsaro, matasan sun yanke shawarar daukar doka a hannunsu, inda suka yi masa duka sannan suka kona shi har lahira.

Shaidu sun ce kokarin wasu dattawan unguwar domin dakatar da matasan bai yi tasiri ba, domin taron ya yi yawa, yayin da babban fushi ya turnuke su.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ba ta fitar da cikakken bayani kan faruwar lamarin ba tukuna, sai dai majiyoyin jaridar ZANCEN YAU247 sun ce an fara bincike kan wannan lamari.

Lamarin ya sake jawo tambayoyi kan yawaitar daukar doka a hannu a wasu yankuna, musamman a lokacin da ake fama da karuwar satar waya da wasu laifuka a birnin Kano.

A halin yanzu, ana ci gaba da bukatar hukumomi su dauki matakan kare rayukan jama’a da kuma hukunta wadanda ke aikata irin wannan danyen aiki.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO