Lamine Yamal: Dan Shekara 18 da Kwallaye 96

Fitaccen matashin dan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya ci gaba da karya tarihin kwallon kafa, domin ya kai 96 gudummawar kwallaye (goals + assists) ga kulob da ƙasa duk yana da shekaru 18 kacal.

Wannan matashi dan baya, wanda ake ganin yana daga cikin manyan hazikan kwallon kafa na zamani, ya hau mataki cikin sauri tun bayan shiga babban tawagar Barcelona da kuma samun gurbi a kungiyar ƙwallon kafar ƙasar Spain. Hanzarinsa, iya kirkira da kuma nutsuwarsa a gaban raga sun sanya shi zama muhimmin ɗan wasa ga kungiyoyin biyu duk da ƙuruciyarsa.

Tarin Yamal ya haɗa da muhimman ƙwallaye, manyan assists, da kuma fitattun wasanni a lokutan da ake buƙatarsa sosai, wanda hakan ya sa duniya ta fara yi masa kallon girmamawa. Masu sharhi da magoya baya na ganin cewa matashin zai iya zama ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasa idan ya ci gaba da irin wannan cigaba.

Da 96 G/A a shekara 18, duniya na ci gaba da kallon yadda ƙwarewar Lamine Yamal za ta kai shi a nan gaba.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO