Kisan Kristoci: Tsauraren Matakai 7 Da Amurka Za Ta Ɗauka Kan Najeriya
Washington, DC — Majalisar Dokokin Amurka ta fitar da wani rahoto mai nauyi da ya kunshi jerin shawarwari guda bakwai da ta ce dole ne Amurka ta ɗauka kan zargin muzgunawa da kashe Kiristoci a Najeriya. Rahoton, wanda aka miƙa wa tsohon shugaban Amurka , ya nuna cewa rikice-rikicen da ake fama da su a Najeriya sun haifar da damuwa a matakin duniya, musamman kan kare ‘yancin addini.
Rahoton ya ce lokaci ya yi da Amurka za ta yi amfani da karfin tsaro, diplomasiyya da tattalin arziki domin matsawa kan waɗanda ke zargin aikata laifukan da suka shafi addini a Najeriya.
1. Takunkumi Ga Masu Laifi Da Ba Za a Iya Kaucewa Ba
Rahoton ya nemi gwamnatin Amurka ta kakaba takunkumi ga duk wani shugaba ko kungiya da aka samu da hannu a hare-haren da suka shafi addini.
Ana sa ran cewa hakan zai zama darasi ga manyan masu rike da mukaman gwamnati da kungiyoyin da ake zargi.
2. Hana Biza Ga Wadanda Ake Zargi
Majalisar ta nemi a haramta ko a takaita visa ga mutanen da ake zargi da aikata kisan addini ko taimaka masa. Wannan zai shafi jami’an gwamnati, shugabannin al’umma da sauran masu tasiri.
3. Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro
Rahoton ya bukaci a ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya. Wannan ya haɗa da:
- Horas da jami’an tsaro
- Musayar bayanan leƙen asiri
- Faɗaɗa kayan aiki domin yaƙar ayyukan ta’addanci
Rahoton ya nanata muhimmancin dakile ayyukan da .
4. Duba Dokokin Shari’a Da Na Cin Mutuncin Addini
Rahoton ya yi kira da a sake duba dokokin Shari’a da jihohin arewa ke amfani da su. Ta ce dokokin na iya cutar da ‘yancin addini tare da haifar da hukunci da basu dace ba.
5. Yarjejeniyar Tsaro Ta Musamman
Shawarwarin sun haɗa da bukatar samar da yarjejeniyar tsaro ta musamman tsakanin Najeriya da Amurka domin yaƙar ta’addanci tare da kare al’ummomi da ke fama da hare-hare.
6. Haɗin Kai Da Kasashen Turai
Rahoton ya nemi Amurka ta yi aiki tare da wasu ƙasashen Turai domin cin ma wadannan manufofi.
Wannan a cewar rahoton, zai ƙara matsin lamba ta fuskar diplomasiya domin tabbatar da kare ‘yancin addini a Najeriya.
7. Amfani da Tattalin Arziki Wajen Matsawa Kan Kungiyoyin da Ke Da Haɗari
Rahoton ya ce ana iya amfani da matakan tattalin arziki, ciki har da takaita wasu kayayyakin noma da kiwo, domin matsawa kan kungiyoyin makiyaya masu dauke da makamai.
Comments
Post a Comment