Kanté da En-Nesyri Sun Gaza Sauya Sheƙa Bayan FIFA Ta ƙi Amincewa da Ƙarar Fenerbahçe da Al Ittihad
Rahotanni sun nuna cewa duka ƙungiyoyin sun yi imani cewa sun cimma matsaya ta baki da ‘yan wasan kuma suna dab da kammala cinikayen. Sai dai matsalar ta taso ne lokacin da takardun da ake buƙata ba su cika ka’ida ba ko kuma ba a tura su akan lokaci ba — kuskuren gudanarwa da ya lalata komai.
FIFA ta duba ƙarar da aka shigar cikin gaggawa, amma ta yanke hukuncin cewa ba za a amince da wadannan canje-canjen ba, domin ba su kai matsayin cikakken kammalawa ba, wato matakin “here we go” kamar yadda Fabrizio Romano ke nuni da hakan a lokutan da cinikaye ya kammala.
Rashin amincewar ya nuna cewa:
- Kanté zai cigaba da kasancewa a Al Ittihad, duk da yunkurin da Fenerbahçe ta yi na kawo shi kafin rufe tagar cinikaye.
- En-Nesyri zai cigaba da zama a Sevilla, bayan Al Ittihad ta gaza cimma yarjejeniya da shi.
Rushewar wadannan cinikaye biyu babbar matsala ce ga ƙungiyoyin da abin ya shafa, musamman ganin cewa duka biyun sun nemi ƙarfafa wasu muhimman matsayi a cikin tawagarsu a wannan kakar. Hakan ya kuma tayar da tambayoyi game da yadda suka gudanar da harkokin cikin gida da kuma kulawa da takardu.
Yanzu da tagar cinikaye ta rufe, Fenerbahçe da Al Ittihad za su koma da mayar da hankali kan ‘yan wasan da suke dasu wajen ci gaba da fafutukar wannan kakar.
Comments
Post a Comment