El-Rufai Yayi Zargin Ofishin Nuhu Ribadu Ya Shigo da Gubar thallium sulphate Wannan Kasa

An samu tashin hankali a fagen tsaro bayan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fallasa wani zargi mai nauyi kan Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) ƙarƙashin NSA Nuhu Ribadu.

A cewar El-Rufai, ONSA ta sayi kilo 10 na sinadarin thallium sulphate – wani guba mai ƙarfi, marar wari, kuma mai matuƙar hatsari ga rayuwar ɗan adam. Ya ce an samo sinadarin ne daga ƙasar Poland, kuma yana buƙatar cikakken bayani domin lafiyar al’umma.

El-Rufai ya aika wa NSA Ribadu wasiƙa a ranar 30 ga Janairu, 2026, inda ya nemi a bayyana:

  • Me za a yi da wannan guba mai haɗari?
  • Wace hukuma ta bayar da izinin shigo da shi?
  • A ina aka adana shi, kuma wane matakin tsaro aka ɗauka?
  • Shin NAFDAC da NCDC sun shiga cikin tsarin izini da bincike?
  • Shin an yi nazari kan yiwuwar barazana ga lafiyar jama’a?

El-Rufai ya ce irin wannan sinadari ana amfani da shi ne a takamaiman fannonin bincike ko tsaro, amma yana buƙatar tsauraran ka’idoji saboda yawan haɗarinsa. Ya jaddada cewa jama’a na da ‘yancin sanin gaskiya idan irin wannan abu mai haɗari ya shiga ƙasar.

Har yanzu ofishin na mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro bai fitar da wata sanarwa ba kan zargin da ake yi, lamarin da ya ƙara tayar da kura a cikin al’umma.

Za mu ci gaba da kawo muku cikakkun bayanai yayin da labarin ke ƙara bunƙasa.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO