EFCC Ta Kama Jarumar Kannywood, Samha Inuwa Bisa Zargin Wulakanta Naira

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), reshen Kano, ta kama sananniyar jarumar Kannywood Samha Inuwa bisa zargin bata darajar Naira.

A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Talata, 3 ga Fabrairu, 2026, an cafke jarumar ne bayan wani faifan bidiyo ya karade kafafen sada zumunta, inda aka ganta na goge majina daga hancinta da takardun Naira — abin da doka ta haramta bisa tanadin dokar Babban Bankin Najeriya (CBN).

Jami’an EFCC sun kaddamar da bincike nan da nan bayan bidiyon ya yi kamari, inda suka bibiyi inda take suka kuma kama ta domin yi mata tambayoyi. Yanzu haka tana tsare a ofishin hukumar da ke Kano yayin da ake ci gaba da bincike.

Wani jami’in EFCC ya tabbatar da cewa za a gurfanar da Inuwa a kotu bayan kammala bincike.

Lamarin ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya, inda jama’a da dama ke sukar wannan aiki tare da kira ga hukuma da ta kara tsananta matakan hukunta masu bata darajar Naira.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO