Atiku da Seyi Makinde Sun Kai Ziyarar Boye Gidan IBB a Minna
Atiku ya isa Minna ne da tsakar rana, kimanin 1:30 pm, inda ya nufi gidan IBB kai tsaye. Gwamna Makinde ya bi sahu daga baya, suka dunguma zuwa wani taron sirri da ke dauke hankulan jama’a, lamarin da ya sa ake ta fassarori kan dalilin zuwan manyan shugabannin biyu tare.
A halin yanzu, ba a bayyana dalilin taron ba, domin taron ya gudana ne a boye ba tare da bayani ga manema labarai ba. Hakazalika, babu wata sanarwa da bangaren Atiku, gwamnatin Oyo ko iyalan IBB suka fitar dangane da abin da aka tattauna.
Sai dai masu sharhi kan siyasa na ganin cewa irin wannan ziyarar ta yi kama da shirye-shiryen sassanta matsalolin cikin jam’iyyar PDP, ko kuma neman shawarwari daga jiga-jigan siyasa ganin yadda ake shirin murza ledar siyasa a kasar nan.
Gidan IBB dai ya kasance wuri da manyan ‘yan siyasa ke yawan ziyarta domin neman shawarwari ko goyon baya musamman kafin manyan zabe ko muhimman yanke shawara.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, taron na ci gaba da daukar hankali, kuma ana sa ran za a samu karin bayani idan an fitar da cikakken jawabi daga daya bangare.
Comments
Post a Comment