ABIN DA YA FARU TSAKANIN ATIKU DA GWAMNAN OYO, SEYI MAKINDE, A MINNA
Ganawar, wadda aka shirya a cikin tsauraran matakan sirri, ta tattara manyan batutuwa da suka shafi makomar siyasar Najeriya, musamman rawar da jam’iyyar ADC za ta taka a zaben 2027.
ME YA SA AKA YI GANAWAR?
Bayanan da suka fito daga majiya kusa da taron sun nuna cewa an zaɓi wuri da mahalarta ne bisa tsari mai zurfi domin tabbatar da amincewa, sirri da karɓuwa daga dukkan ɓangarori. Wani babban batu da aka tattauna shi ne rashin yuwuwar Peter Obi ya amince ya zama mataimakin Atiku, ko kuma Arewa ta karɓi Obi a matsayin wanda zai gaji Atiku idan ya lashe zaɓe.
ATIKU NA GAB DA SAMUN TAKARAR ADC – WATA MAJIYA
Rahotanni sun nuna cewa Atiku na da tabbacin kashi 70% na samun tikitin takarar shugabancin ƙasa a ADC, sakamakon rawar da ya taka wajen ganin an cire tsarin ware takara ga yankuna (zoning) a jam’iyyar.
MAKINDE YA AMINCE YA SAKE SHEKARWA – AMMA DA SHARADI
Majiyar ta kara da cewa Gwamna Makinde ya amince ya koma jam’iyyar ADC ne bisa sharadin cewa za a ba shi kujerar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku. Wannan bukata za a gabatar wa da manyan kusoshin Atiku domin tattaunawa da tabbatarwa nan gaba.
TALLAFIN N10BN DA TSARE-TSAREN ZABE
Makinde ya kuma yi alkawarin bayar da Naira biliyan 10 a matsayin tallafin farko ga jam’iyyar ADC, wanda za a biya a matakai biyu. Ya kuma ce zai ƙara wasu kuɗade yayin da yaƙin neman zaɓe zai fara.
Gwamnan ya yi alkawarin kawo gagarumin tasiri a zaben fidda gwanin ADC, tare da tabbatar da cewa zai samu delegates daga yankin Yammacin Najeriya (Southwest). Haka kuma, ya ce zai yi amfani da tasirin matarsa ’yar asalin Jihar Rivers domin samun kuri’un delegates daga yankin Kudu maso Kudu.
A zaben 2027 kuma, Makinde ya shaida cewa kasancewarsa ɗan takara daga Kudu maso Yamma zai taimaka wajen raba kuri’un yankin, wanda hakan zai ba ADC damar samun rinjaye.
GANAWA TA GABA A DUBAI
An ce an riga an tsayar da wani taro na gaba, wanda za a gudanar a birnin Dubai na ƙasar UAE cikin makonni biyu masu zuwa.
Rahoton ya fito daga tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, wanda ya bayyana abin da ya faru a bayan fage na wannan muhimmin zama.
Za mu ci gaba da bibiyar wannan ci gaba mai zafi a siyasar Najeriya.
Comments
Post a Comment