“Zamfara Ba Ta Taɓa Samun Gwamna Kamar Shi Ba” — Sarkin Fulanin Zamfara Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Dauda Lawal Ya Cancanci Wa’adi Na Biyu
A wani babban bayani da ya girgiza fagen siyasar Zamfara, Sarkin Fulanin Zamfara kuma tsohon ɗan Majalisar Dokoki wanda ya wakilci Maru/Bungudu daga 2019 zuwa 2023, Alhaji Shehu Ahmed, ya bayyana cewa Jihar Zamfara ba ta taɓa samun gwamna mai aiki kamar Gwamna Dauda Lawal ba tun kafuwarta.
Da yake magana a wata tattaunawa ta musamman da jaridar ZANCEN YAU 247, Sarkin Fulanin Zamfara ya ce babu wanda ya dace ya jagoranci jihar a gaba sai Gwamna Dauda Lawal, saboda ayyukan alheri da sauye-sauyen da ya kawo cikin kankanin lokaci.
A cewarsa, ɗaya daga cikin manyan nasarorin da gwamnan ya samu shi ne biyan bashin fansho da giratuti da suka dade suna damun tsofaffin ma’aikatan gwamnati tsawon shekaru.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawal ta gyara kusan dukkan makarantun jihar da aka bari cikin lalacewa, lamarin da ya dawo da martabar ilimi a Zamfara.
A bangaren ababen more rayuwa, Alhaji Shehu Ahmed ya ce titunan jihar — ciki har da hanyoyin karkara — sun samu gyara sosai, yayin da birnin Gusau ya sauya fasali gaba ɗaya.
“Idan mutum bai ziyarci Gusau na dogon lokaci ba, idan ya dawo yanzu ba zai gane titunan ba saboda irin gyare-gyaren da aka yi,” in ji shi.
Sarkin Fulanin Zamfara ya kara da cewa salon mulkin Dauda Lawal ya sha bamban da na dukkan gwamnonin da suka gabata, yana mai jaddada cewa gwamnan na kokari sosai wajen magance matsalar tsaro.
Duk da haka, ya bayyana cewa babban ƙalubalen da gwamnan ke fuskanta shi ne ƙarancin ikon da yake da shi kan ‘yan sanda da sojoji, amma duk da haka yana ta tattaunawa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu domin kawo ƙarshen rashin tsaro a Zamfara.
“Da ace yana da cikakken iko, da an kawo karshen matsalar tsaro tun tuni,” in ji shi.
A karshe, Sarkin Fulanin Zamfara ya bayyana cikakken goyon bayansa kashi 100 cikin 100 ga Gwamna Dauda Lawal, yana mai cewa:
“Dauda Lawal shi ne zabin kowanne gida a Jihar Zamfara. A yau, ana magana da ayyukansa a kowane lungu da sako.”
Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Zamfara ke kara daukar zafi, kuma ana kallon wannan goyon baya a matsayin babbar alama ga makomar siyasar jihar.
Comments
Post a Comment