Yanda Aka Hallaka Mutum 7 ’Yan Gida Guda a Jihar Kano
Jihar Kano ta shiga jimami bayan da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai harin gilla tare da kashe mutum bakwai (7) ’yan gida guda a unguwar Dorayi Chiramchi, dake karamar hukumar Gwale a birnin Kano.
Rahotannin da jaridar ZANCEN YAU 247 ta samu sun nuna cewa lamarin ya faru ne da tsakar dare, inda maharan suka afka cikin gidan iyalan tare da kai musu hari ta hanyar amfani da makamai masu kaifi da kuma bindiga, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dukkan mutanen bakwai a wajen.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana wa jaridar ZANCEN YAU 247 cewa maharan sun shigo cikin unguwar ne a cikin shiru, kafin su kai harin cikin gaggawa, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici da tashin hankali.
Wani mazaunin Dorayi Chiramchi ya shaida cewa:
“Mun wayi gari da mummunan labari. Gaba ɗaya unguwar ta rude, ba mu taba ganin irin wannan ta’asa ba.”
Jami’an tsaro, ciki har da ’yan sanda, sun isa wurin da lamarin ya faru domin fara bincike, tare da kai gawarwakin mamatan zuwa asibiti. Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an fara farautar wadanda ake zargi da aikata wannan kisan gillar.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin harin ba, sai dai ana zargin cewa lamarin na da nasaba da rikicin cikin gida ko kuma wata fitina ta daba.
Gwamnatin jihar Kano da manyan jami’an tsaro sun yi Allah-wadai da wannan mummunan lamari, tare da jaddada aniyar tabbatar da tsaro da kuma ganin an hukunta duk wanda ke da hannu a wannan aika-aika.
Al’ummar Dorayi Chiramchi na kira ga hukumomi da su ƙara tsaurara tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman ganin yadda hare-haren ta’addanci ke ƙaruwa a wasu sassan birnin Kano.
Comments
Post a Comment