’YAN SANDAN KANO SUN KAMA WADANDA AKE ZARGI DA YI WA UWA DA ’YA’YANTA SHIDA KISAR GILLA

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama manyan mutane uku da ake zargi su ne suka shirya tare da aikata mummunan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ’ya’yanta guda shida a unguwar Dorayi Chiranchi, cikin birnin Kano.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Asabar, 18 ga Janairu, 2026, wacce jaridar ZANCEN YAU247 ta samu, ta ce kamen ya biyo bayan umarnin Babban Sufeton ’Yan Sanda na kasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, inda aka yi amfani da bayanan sirri domin cafke wadanda ake zargin.

¹Sanarwar ta bayyana cewa, a karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, jami’an ’yan sanda na musamman sun gudanar da samame daga karfe 10:00 na dare zuwa karfe 4:00 na asuba tsakanin 17 zuwa 18 ga Janairu, inda suka kama:

Umar Auwalu, mai shekara 23, dan Sabuwar Gandu, Isyaku Yakubu (Chebe), mai shekara 40, dan Sagagi, Yakubu Abdulaziz (Wawo), mai shekara 21, dan Sabon Gida Sharada.

Rundunar ta ce shugaban wannan kungiyar, Umar Auwalu, wanda aka tabbatar dan uwa ne ga matar da aka kashe (dan uwanta), ya amsa laifin aikata wannan kisan gilla tare da bayyana cewa su ne suka aikata wasu munanan laifuka a baya, ciki har da kashewa da kona wasu mata biyu a unguwar Tudun Yola, Kano.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin akwai: tufafi hudu masu jinin mutum, wayoyin salula biyu na mamaciyar, adda, gora, kudi da aka sace a wurin, da wasu muggan makamai.

Rundunar ’yan sandan ta ce bincike na ci gaba da gudana domin gano karin bayanai da kuma yiwuwar kama wasu da ke da hannu a lamarin.

A karshe, rundunar ta yaba da kokarin jami’anta tare da godiya ga al’ummar Kano bisa addu’o’i, goyon baya da hadin kai, tana kuma jaddada kudirinta na tabbatar da cewa duk masu aikata laifuka za su fuskanci hukunci bisa doka.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO