Tsoro Ya Mamaye Karkarar Kano Yayin da ’Yan Bindiga Ke Karɓar Haraji Daga Manoma: Gwamnati Ta Karyata
Rahotanni masu tayar da hankali na nuna cewa ’yan bindiga na samun tasiri a wasu yankunan karkara da dazuzzukan Jihar Kano, lamarin da ke haifar da fargaba a tsakanin manoma da mazauna yankunan da abin ya shafa.
Bincike da ZANCEN YAU ya gudanar ya nuna cewa ’yan bindigar na fakewa a dazuzzuka kamar Falgore, inda ake zarginsu da karɓar haraji daga manoma, tsoratar da jama’a, da hana noma sai an biya kuɗin kariya.
Sai dai Gwamnatin Jihar Kano ta karyata jita-jitar mamaye jihar, tana mai cewa babu wani gari ko karamar hukuma da ta fadi, kuma matsalar na faruwa ne a kan iyaka da dazuzzuka, inda ’yan bindiga daga jihohin makwabta ke kutsowa.
Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da kai farmaki da samamen tsaro, tare da gargadin jama’a da su guji yadawa ko yarda da labaran ƙarya.
Duk da haka, mazauna yankunan karkara na cewa akwai wuraren da ba za a iya shiga ba sai da yardar ’yan bindiga, abin da ke nuna barazana mai bukatar daukar matakin gaggawa.
Comments
Post a Comment