Najeriya Za ta Fara Amfani da Tsarin Kudi Na Musulunci Wajen Ba da Rahoton Kudi A Kasar
Hukumar kula da rahotannin kudi ta Najeriya, wato Financial Reporting Council of Nigeria (FRC) ta bayyana cewa tana kan hanyarta ta shigar da kaidojin kuɗin Musulunci na duniya (Islamic finance standards) cikin Tsarin Rahoton Kuɗi na Najeriya (Nigerian Financial Reporting Framework – NFRF), a wani yunkuri da ake ganin zai ƙarfafa gaskiya, daidaito, da karɓuwar tsarin kuɗin ƙasar a matakin duniya.
Rahotannin da su ka iso hannun ZANCEN YAU247 sun nuna cewa wannan shiri na FRC zai bai wa bankunan Musulunci, kamfanonin kuɗi, da sauran cibiyoyin da ke aiki bisa tsarin Shari’ar Musulunci damar gabatar da rahotannin kuɗinsu bisa ka’idoji da duniya ke amincewa da su, ba tare da sabani da dokokin Najeriya ba.
A cewar FRC, shigar da waɗannan ka’idoji zai taimaka wajen ƙara jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje, musamman daga kasashen da tsarin kuɗin Musulunci ya yi karfi kamar Gabas ta Tsakiya da wasu sassan Asiya. Haka kuma, ana sa ran matakin zai inganta amincewa da tsarin rahoton kuɗi na Najeriya a idon hukumomin ƙasa da ƙasa.
Wasu masana harkokin hada-hada da kuɗi, wadanda jaridar ZANCEN YAU24 ta zanta da su sun sun bayyana cewa wannan yunƙuri zai buɗe sabon babi ga kasuwar kuɗin Musulunci a Najeriya, tare da ba wa kamfanoni damar samun sauƙin bin ka’idoji guda ɗaya da ake amfani da su a kasuwannin duniya. Sun kuma ce hakan zai rage ruɗani da sabani da ke tasowa wajen rahoton kuɗi tsakanin tsarin gargajiya da na Musulunci.
Sai dai wasu masanan sun jaddada bukatar hukumar ta gudanar da cikakken shawarwari da masu ruwa da tsaki, ciki har da bankuna, masu lissafin kuɗi, da hukumomin sa ido, domin tabbatar da cewa aiwatar da sabon tsarin bai haifar da cikas ga tsarin kuɗin da ake amfani da shi a yanzu ba.
Ana sa ran FRC za ta fitar da ƙarin bayanai kan jadawalin aiwatar da wannan shiri da kuma yadda za a haɗa ka’idojin cikin NFRF, yayin da al’umma da masu ruwa da tsaki ke sa ido kan yadda wannan mataki zai sauya fasalin rahoton kuɗi da kasuwar kuɗin Musulunci a Najeriya.
Comments
Post a Comment