Najeriya Ta Dauki Muhimmin Mataki na Nuna wa Duniya Kokarinta na Kare Al'ummar Kiristoci

A wani mataki na gaba-gaba domin kara fahimtar kokarinta na tsaro da kuma karfafa dangantakar kasa da kasa, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dauki hayar wani fitaccen kamfanin lobbiyanci da hulda da jama’a da ke Amurka domin bayyana matakan da take dauka na kare al’ummomin Kirista tare da yakar tsattsauran ra’ayi da tashin hankali a fadin kasar.
A karkashin kwangilar da ta kai dala miliyan 9, wadda aka aiwatar ta hannun kamfanin Aster Legal mai hedkwata a Kaduna a madadin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, kamfanin DCI Group da ke Washington zai rika hulda da ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a Amurka domin gabatar da matsayar Najeriya kan sabbin damuwar da aka taso a Washington.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar 17 ga Disamba, 2025, inda ta tanadi aikin hadin gwiwa na tsawon watanni shida — tare da yiwuwar tsawaitawa — wanda a cikinsa kamfanin zai taimaka wajen isar da kudurin gwamnatin tarayya na kare dukkan ‘yan kasa, ciki har da al’ummomin Kirista, tare da kara karfafa hadin gwiwa a yaki da kungiyoyin jihadi da sauran barazanar tsaro a fadin Yammacin Afirka.
Tsarin kwangilar, kamar yadda ZANCEN YAU ta gano, ya hada da biyan gaba na dala miliyan 4.5 da kuma kudin aiki na wata-wata, lamarin da ke nuna kudurin Najeriya na tabbatar da cewa labarinta da ayyukanta sun samu fahimta daidai daga abokan hulda na kasa da kasa.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa ZANCEN YAU cewa jami’an gwamnati sun jaddada cewa wannan shiri na daga cikin manyan dabarun diflomasiyya da ake bi domin ci gaba da samun muhimmiyar goyon bayan Amurka ga ayyukan tsaron Najeriya, tare da nuna irin matakan da kasar ke dauka na kare al’ummomi masu rauni da inganta zaman lafiya.
Wannan ci gaba, kamar yadda ZANCEN YAU ta fahimta, ya samu karbuwa daga masu lura da al’amura da dama, wadanda ke kallonsa a matsayin yunkuri na diflomasiyya mai hangen nesa, wanda ke nuna shirye-shiryen Najeriya na yin mu’amala cikin gaskiya kan batutuwan tsaro, ‘yancin addini, da hadin gwiwar kasa da kasa.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO