Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Yi Gargaɗin Barazanar Yunwa Mai Tsanani a Najeriya
Abuja — Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta yi gargaɗi cewa Najeriya na fuskantar barazanar yunwa mai tsanani ƙwarai (“catastrophic”), sakamakon ƙarancin kuɗaɗen tallafin abinci da ke ƙara ƙarewa.
Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya ce miliyoyin ’yan Najeriya masu rauni na iya rasa damar samun tallafin ceto rayuwa a watanni masu zuwa, muddin ba a samu kuɗaɗen gaggawa ba. Hukumar ta kiyasta cewa fiye da mutane miliyan 35 na iya fuskantar matsanancin ƙarancin abinci a shekarar 2026, musamman a yankunan arewa da rikice-rikice suka fi shafa.
Ƙaruwa a matsalar tsaro, hauhawar farashi, da ƙauracewar jama’a daga muhallansu sun ƙara tsananta halin da ake ciki, lamarin da ya sa UN ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da masu ba da tallafi na ƙasashen waje da su dauki matakin gaggawa domin kauce wa afkuwar bala’in jin-ƙai.
Comments
Post a Comment