Kwankwaso Ya Bayyana Yiwuwar Shiga Hadakar ADC

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana yiwuwar shiga hadakar jam’iyyar ADC a wani sabon lamari da ya tayar da cece-kuce a fagen siyasar Najeriya.

Kwankwaso ya yi wannan jawabi ne yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan matsin lambar da ake masa na ya jagoranci wasu magoya bayansa zuwa jam’iyyar APC. Sai dai jagoran na NNPP ya yi watsi da hakan, yana mai cewa ba zai taba shiga jam’iyyar da ya zarga da “lalata Najeriya” ba.

A cewarsa:
“Maimakon a rika kira gare mu da mu jagoranci mutane zuwa APC, da zamu fi son mu shiga ADC – sabuwar jam’iyya – fiye da shiga jam’iyyar da ta lalata Najeriya.”

Jawabin nasa ya sake bude sabuwar fassara ga makomar siyasar NNPP da kuma dangantakar jam’iyyar da sauran manyan jam’iyyun kasar. Har yanzu babu cikakken bayani ko Kwankwaso zai bar NNPP gaba ɗaya ko kuwa hadin kan siyasa ne kawai da ADC.

Wani manazarcin harkar siyasa ya shaida wa jaridar ZANCEN YAU24 cewa wannan na iya canza taswirar siyasar 2027, musamman duba da tasirin Kwankwaso a Arewa maso Yamma da kuma irin gagarumin karbuwa da yake da shi wajen matasa.

A halin yanzu dai jam’iyyun siyasar kasar na jiran matakin da za su dauka daga bangarensa, yayin da magoya bayansa ke ta nuna goyon baya kan dukkan zabin da zai yi a gaba.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO