Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Dakatar da Yajin Aiki, tare da Ba Gwamnati Wa'adi
Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa, (National Association of Resident Doctors – NARD) ta sanar da dakatar da shirin yajin aikin kasa baki ɗaya da ta yi niyyar fara wa a yau Litinin, 12 ga Janairu, 2026.
Sanarwar dakatarwar ta biyo bayan taron gaggawa na shugabannin ƙungiyar (Emergency NEC) da aka gudanar a daren Lahadi, inda aka yi nazari kan halin da tattaunawa da gwamnatin tarayya ta kai.
Dalilan Dakatar da Yajin Aikin
A cewar ƙungiyar, an dakatar da yajin aikin ne sakamakon:
Alƙawuran da gwamnatin tarayya ta sake bayarwa na warware manyan matsalolin da ke addabar likitocin;
Shiga tsakani daga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tattaunawa tsakanin NARD da manyan jami’an gwamnati;
Da kuma umarni na wucin gadi daga Kotun Masana’antu ta Kasa, wanda ya hana fara yajin aikin har sai an saurari shari’ar da ke gaban kotu.
Kungiyar ta bayyana cewa wannan mataki ba janye yajin aiki gaba ɗaya ba ne, illa dai dakatarwa domin bai wa gwamnati damar nuna gaskiya ta hanyar aiwatar da alkawuran da ta dauka.
NARD ta ce za ta sake nazari kan halin da al’amura suka kai a taron NEC na gaba da aka shirya yi a karshen Janairu, inda za a tantance ko gwamnati ta fara cika bukatun likitocin ko a’a.
Idan aka gaza ganin gagarumin ci gaba, ƙungiyar ta yi gargadin cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakan da suka dace, ciki har da komawa yajin aiki.
Daga cikin manyan bukatun da likitocin ke nema akwai:
inganta albashi da alawus-alawus,
warware matsalar jinkirin biyan hakkoki,
da kuma kyautata yanayin aiki a asibitocin gwamnati.
Dakatar da yajin aikin ta kawo sauƙi ga marasa lafiya da iyalansu, musamman a manyan asibitocin koyarwa da na gwamnati, inda ake fargabar durƙushewar ayyukan lafiya idan yajin aikin ya gudana.
Masu lura da al’amura na ganin cewa wannan dakatarwa jarabawa ce ga gwamnatin tarayya, wadda za ta nuna ko tana da niyyar magance matsalolin bangaren lafiya ko kuwa rikici zai sake dawowa.
Comments
Post a Comment