Kasar Japan Ta Sake Kunna Babbar Tashar Nukiliyarta

Kasar Japan ta sake kunna wani matattarar makamashin nukiliya a babbar tashar nukiliya mafi girma a duniya, kusan shekaru 15 bayan ibtila'in da ya auku a tashar Fukushima a shekarar 2011, wanda ya tilasta wa ƙasar rufe dukkan matattarar nukiliyarta.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin Japan na ƙara hanyoyin samar da wutar lantarki tare da rage dogaro da makamashin mai da iskar gas da ake shigo da su daga ƙasashen waje. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar hauhawar farashin makamashi a duniya.

An rufe tashoshin nukiliyar Japan baki ɗaya ne bayan girgizar ƙasa da ambaliyar ruwa (tsunami) da suka afku a arewa maso gabashin ƙasar, lamarin da ya haddasa mummunar matsala a tashar Fukushima Daiichi. Wannan ibtila'i ya haifar da fargaba a cikin al’umma game da tsaron amfani da makamashin nukiliya.

Sai dai hukumomin Kasar Japan sun ce an aiwatar da tsauraran matakan tsaro da sabbin ka’idoji kafin sake kunna wannan matattarar, domin tabbatar da kare rayuka da muhalli. Sun jaddada cewa an gudanar da bincike mai zurfi da gwaje-gwaje da dama kafin a ba da izinin sake fara aiki.

Masana harkar makamashi na ganin cewa sake kunna tashoshin nukiliya zai taimaka wa Japan wajen tabbatar da wadatar wutar lantarki da kuma cimma burin rage hayakin da ke gurbata muhalli. Duk da haka, wasu kungiyoyin fararen hula na ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar barazanar tsaro da illa ga muhalli.

Ana sa ran cewa wannan mataki zai haifar da muhawara mai zafi a cikin gida da kuma hankalin kasashen duniya, musamman ganin irin tasirin da bala’in Fukushima ya yi a tarihin amfani da makamashin nukiliya a Kasar Japan.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO