EFCC Ta Kwato ₦aira Miliyan 802m daga cikin ₦aira Biliyan 1.3bn da Banki Yayi Kuskuren Tura wa wani Mutum
Wani lamari mai tayar da hankali ya girgiza Najeriya bayan da wani banki ya tura kuɗi har ₦1.3 biliyan bisa kuskure zuwa asusun wani mutum, wanda ake zargin ya fara watse kuɗaɗen kafin a gano lamarin.
Binciken da ZANCEN YAU 247 ya gudanar ya nuna cewa kuskuren ya faru ne sakamakon matsalar tsarin banki, amma kafin bankin ya gano abin da ke faruwa, mai asusun ya riga ya kashe wani bangare na kuɗin, ciki har da rarraba wa wasu mutane da kuma yin wasu ayyuka da su.
Majiyarmu ta tabbatar cewa Hukumar EFCC ta ɗauki mataki cikin gaggawa, ta bi sahun kuɗin, inda ta kwato kusan ₦802 miliyan, duk da cewa ba a samu damar kwato duka kuɗin ba.
Rahotannin da ZANCEN YAU 247 ya bibiya sun gano canja wuraren kuɗi zuwa asusun dangi da abokai, an yi kashe-kashe na gaggawa kafin a rufe hanyoyin cirar kuɗi
Majiyarmu ta kara da cewa tuni aka gurfanar da wanda ake zargi da wasu mutane a kotu
ZANCEN YAU 247 ya tuntubi masana shari’a, inda suka jaddada cewa: “Kuɗin da ba naka ba, haramun ne ka taɓa shi.”
Sun kara da cewa doka ta bayyana cewa duk wanda ya yi amfani da kuɗin da ya san ba nasa ba na iya fuskantar tuhumar sata da damfara, ko da kuskuren banki ne.
Masanan sun Kuma shawarci al'umma cewa idan hakan ta faru kada mutum ya cire ko kashe kuɗin, ya sanar da bankinsa nan take, domin kare kai daga matsalar doka da kunya.
Comments
Post a Comment