An yanke wa Wanda ya Kashe Tsohon Firayim Ministan Japan, Hukuncin Daurin Rai_da-rai
Kotun Japan ta yanke wa mutumin da ya kashe tsohon Firayim Ministan ƙasar, Shinzo Abe, hukuncin daurin rai-da-rai.
Hakan ya biyo bayan kammala shari’ar da ta ɗauki tsawon shekaru, wadda ta girgiza ƙasar Japan baki ɗaya, kamar yadda gidan talabijin na gwamnati, NHK, ya ruwaito.
An dai kashe Shinzo Abe ne ta hanyar amfani da bindiga da aka ƙera da hannu, lamarin da ya ba mutane da dama mamaki matuƙa, ganin cewa hare-haren bindiga abu ne da ba kasafai ake samu a Japan ba sakamakon tsauraran dokokin mallakar makamai.
Hukuncin da kotu ta yanke ya kawo ƙarshen shari’ar da ta ja hankalin duniya, inda ta kuma jefa haske kan wata ƙungiyar addini mai ƙarfi wadda ake zargin ta taka rawa a dalilan da suka sa aka aikata wannan mummunan aiki.
Kisan gillar Shinzo Abe ya faru ne yayin da yake gabatar da jawabi a bainar jama’a, lamarin da ya haifar da alhini da Allah-wadai daga shugabanni da jama’a a sassan duniya.
Abe, wanda ya taba rike mukamin Firayim Minista na tsawon lokaci, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun shugabannin siyasar Japan a zamaninsa.
Masana na ganin cewa hukuncin da aka yanke zai zama darasi mai ƙarfi ga duk wanda ke tunanin aikata irin wannan laifi, tare da ƙara tabbatar da matsayar Japan na tsaurara tsaro da adalci a harkokin shari’a.
Comments
Post a Comment