Ɗan Kwankwaso Ya Ajiye Aiki a Matsayin Kwamishina

Ɗan tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi murabus daga muƙaminsa na Kwamishina a Gwamnatin Jihar Kano, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar jihar.

Majiyoyi daga cikin gwamnati sun tabbatar wa jaridar ZANCEN YAU247 cewa murabus ɗin ya samu karɓuwa, duk da cewa har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan dalilan da suka sa ya yanke wannan shawara ba. Sai dai wasu na ganin cewa matakin na iya kasancewa yana da alaƙa da sabbin sauye-sauye da ake samu a siyasar Kano da kuma bambancin ra’ayi a cikin gwamnatin jihar.

Murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauye a harkokin siyasa, musamman a jam’iyyar NNPP da ke mulkin jihar Kano. Wasu masu sharhi na siyasa sun shaida wa jaridar ZANCEN YAU247 cewa ficewar ɗan Kwankwaso daga mukamin na iya yin tasiri ga tsarin tafiyar gwamnati da kuma dangantakar da ke tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa ta musamman domin yin karin haske kan murabus ɗin ba, haka nan shi ma ɗan Kwankwaso bai bayyana ra’ayinsa a bainar jama’a ba.

Masu bibiyar al’amuran siyasa na ci gaba da sa ido kan yadda wannan mataki zai shafi makomar siyasar Kano, musamman dangane da rawar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke takawa a matakin jiha da na ƙasa baki ɗaya.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO