An kai wa Wakiliya Ilhan ta Amurka Hari da Ruwan Guba
Minneapolis, Amurka — A ranar Talatar 27 ga Janairu, 2026, an kai wa Wakiliyar Jihar Minnesota, ta Kasar Amirka, Ilhan Omar, hari a lokacin da take jagorantar taron jama’a a birnin Minneapolis yayin da wani mutum ya garzaya gare ta ya zuba mata wani abu mai ba a sani ba daga wani karamin na’ura mai kama da syringe, yayin da take magana a gaban taron.
Mutumin, wanda ake zargin ya yi hakan da nufin kawo cikas ga taron, nan take an kama shi sannan ‘yan tsaro suka ja shi kasa, suka sa masa hannu bayan sannan aka mika shi ga ‘yan sanda. Jama’ar taron sun yi ta nuna damuwa da mamaki, inda wasu daga cikin wadanda ke taron suka ce abin ya na da wari sosai.
Ilhan Omar ba ta ji rauni ba, duk da cewa ta yi dan kadan kamar an firgita ta, sannan ta ci gaba da jawabin nata ba tare da ta bar taron ba. Ta bayyana cewa ba za a tsorata da irin wannan abu ba, tana mai cewa: “Ba za su hana mu aikata abin da muke yi ba.”
Kafin harin, Omar tana jawabi ne kan batun rufe hukumar kula da shige da fice ta ICE a Amurka tare da kiran sakataren hukumar tsaro ta cikin gida, Kristi Noem, ta yi murabus.
Wannan taron ya zo ne a daidai lokacin da ake karuwar zanga-zanga da tashin hankali kan batutuwan shige da fice a Minneapolis ta Amurka.
‘Yan sanda sun tabbatar da kama wannan mutumi tare da tuhumarsa da laifin yi wa wakiliyar hari a mataki na uku yayin da suke cigaba da bincike kan abin da aka zuba mata. Har yanzu ba a bayyana a fili ko wani hukunci ya fara aiwatarwa ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da gudanar da bincike.
Wannan lamari ya jawo ma ta tagomashi gami da adawa daga ‘yan siyasa daban-daban, inda wasu suka yi tir da irin wannan tashin hankali a harkokin siyasa yayin da wasu suka nuna damuwa kan yadda ake nanata barazanar a tsakanin al’umma.
Comments
Post a Comment